′Yan gudun hijira na wahala a Najeriya | Zamantakewa | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

'Yan gudun hijira na wahala a Najeriya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin duniya ta bayyana damuwa kan ci gaba da karuwar mutanen da suka rasa matsugunansu saboda rigingimu a Najeriya.

Hukumar ta ce wadannan mutane na fuskantar matsaloli na rashin wadatar kayan bukata, abin da ta ce yana da hadarin gaske ga kasar. Wannan sabon adadi na yawan mutanen da suka rasa muhallan nasu da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ta ce ya daga mata hankali, musamman duba da rashin wani shiri na zahiri ga kungiyoyin agaji ta yadda za su iya fuskantar wannan matsala da sannu a hankali ta zama bala'in da ya afkawa al'umma musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Halin ko in kula ga 'yan gudun hijira

Damuwa a kan hali na ko in kula da masu bada tallafai ke nunawa duk da kallon da ake wa Najeriya na kasa mai karfin tattalin arziki a yankin Afrika ta Yamma, ko wane hadari hakan ke da shi? Mrs Angele Dikongue Atangana ita ce wakiliyar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majaisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar Ecowas ta kuma ce...

Kungiyoyin bada agaji ga 'yan gudun hijira a Najeriya

Kungiyoyin bada agaji ga 'yan gudun hijira a Najeriya

"Idan har ba'a dauki mataki na gaggawa ba, za mu iya fuskantar babbar matsala. Mata da yara kanana za su iya kara shiga cikin mumunan hali, shi yasa nake magana a kan gallazawa ta jinsi domin za'a iya sanya yara shiga cikin aiyukan kai hare-hare, don haka ya zama dole mu hanzarta daukar matakan inganta tallafawa mutanen da suka rasa muhallansu."

An dai tabo batun kudurin Kampala da Najeriya ta sanya hannu a kai amma har yanzu ba ta kai ga kafa dokar aiwatar da shi ba, wanda zai tillasta mata samawa mutanen da suka rasa muhallansu mafita ba wai tallafin bargo da Sabulu sannan a mance da su ba. Umar Abdu Mairiga shine jami'in tsare-tsare na kungiyar agaji ta Red Cross ya bayyana damuwa a kan halin da mutanen da suka rasa muhallansu ke ciki.

Raba kayan agaji ga 'yan gudun hijira a Najeriya

Raba kayan agaji ga 'yan gudun hijira a Najeriya

Yace: "A gaskiya suna cikin wani mawuyacin hali kuma sai Allah ne kadai zai iya sama masu maslaha, domin in ka lura mu a Najeriya wadanda suka rasa mahallansu ba wani matsuguni ake sama musu ba, domin a yanzu haka akwai mutanen da suka shiga irin wannan hali shekaru goma kuma ba abinda aka yi musu. Amma bisa abin da muke gani duka wadannan kungiyoyin na agaji suna kokari, amma dai a gaskiya muna yi a makare."

Wane mataki gwamnati ke dauka?

To shin me gwamnatin Najeriya ke yi ne a kan wannan matsala da wasu ke ganin ta kama hanyar fin karfinta? Hajiya Amina Ibrahim BB Faruq ita ce ta wakilci hukumar kula da ‘yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu a Najeriyar.

"Gaskiya ba abin da za mu iya yi mu kadai bane dole sai da tamakonsu, kuma dole ne mu jajirce a kan wannan domin bamu kadai bane ke da irin wannan matsala, amma dai ana kokari a fannin gwamnati."

A yayin da yawan mutanen da suka rasa muhallansu ke ci gaba da karuwa, akwai wadanda gwamnatin ba ta san da zamansu ba, da suka gudu zuwa jihohi da a yanzu suma suka fada cikin rikici kamar jihar Nasarawa, a wani yanayi na garin gudun gara an fada zago.