'Yan gudun hijira 47 sun sauka Italiya
January 31, 2019Talla
Kungiyar agaji ta Sea-Watch ta kasar Jamus ta sauke 'yan gudun hijirar da ta ceto duk da barazanar da ministan cikin gidan kasar ta Italiya Matteo Salvini ya yi wa mata na gurfanar da ita a gaban kuliya idan ta kuskura ta shigo da wadannan 'yan gudun hijira.
An dai karbi 'yan gudun hijirar ne a cikin wasu runfunan tanti wadanda kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta kafa a birnin na Catane. Tun a ranar 19 ga wannan wata na Janeru ne dai wannan jirgin ruwan dauke da 'yan gudun hijira ke yawo a saman teku yana neman samun izinin sauke su a kasar ta Italiya.
A nan gaba ne dai za a rarraba wadannan 'yan gudun hijira 47 a tsakanin kasashen Turai bakwai na Faransa da Potugal da Jamus da Malta da Luxemburg da Romaniya.