1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan Boko Haram na komawa arewa maso yamma

September 24, 2021

Sama da mayaka 200 na kungiyar Boko Haram na barin tushensu domin komawa jihohin Najeriya da ke fama da rigimar 'yan fashin daji da kuma masu garkuwa da mutane.

https://p.dw.com/p/40pTN
Boko Haram
Hoto: Java

Wasu majiyoyin soji a Najeriya, sun ce mayakan Boko Haram masu yawa sun kaura daga tushensa da ke arewa maso gabashin kasar domin hadewa da 'yan bindiga da ke a yankin arewa maso yamma.

Majiyoyin sojin na Najeriya, sun ce wasu kwamandoji biyu ne daga bangaren na Shekau ke jagorantar ayari mai mayaka akalla 250 da ke kan hanyar shiga dajin Rijana da ke cikin jihar Kaduna.

Tururuwar da mayakan na Boko Haram ke yi domin shigewa cikin 'yan bindigar arewa maso yammacin na Najeriya dai, zai kara ta'azzara matsalar sace-sacen dukiyoyi da ma garkuwa mutane domin neman kudin fansa.

Galibin 'yan Boko Haram din dai, mayaka ne da ke a bangaren Abubakar Shekau wanda ya mutu cikin watan Mayun da ya gabata.

Mayakan na Shekau na fuskantar matsala daga mayakan ISWAP karkashin jagorancin Abu Mus'ab al-Barnawi, inda suke neman da su mika musu makamansu.