Yakin duniya na biyu ya cika shekaru 80 | Siyasa | DW | 01.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin duniya na biyu ya cika shekaru 80

Gwamnatin 'yan Nazi ta Jamus karkashin jagorancin Adolf Hilter ta kai harin a kan kasar Poland wanda ya kasance shi ne mafarin barkewar yakin duniya na biyu sakamakon martanin kasashen Ingila da Faransa ga 'yan nazi.

Sojojin Nazi sun yi kaca-kaca da garuruwa da dama  na Poland tare da haddasa babbar asara ta rayukan jama'a, sai dai da yawa daga cikin  Jamusawan ba su labarin barnar da Jamus ta haddasa a kan kasar ta Ploland sai wasu kalilan, duk da yake ministan harkokin waje na Jamus Heiko Maas a lokacin wata ziyarar a Ploland ya amince da cewar Jamus ta yiwa kasar babbar barna a yakin duniyar na biyu.

Masana kamar Farfesa Martin Aus Masanin tarihi a Jamus na cewa, Poland ba wai ta kasance kasa ta farko da Jamus ta mamaye a yakin duniya na biyu ba kawai, ita ce ke da al'umma mafi yawa da suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu.

Tun daga shekara ta 1945 Jamus da Poland ba su da  wata cikakkiyar hulda a tsakaninsu,  sai a lokacin zuwan gwamnatin Willy Brand a shekara ta 1970 wanda ya kai ziyara a Poland kuma har zuwa shekara ta 1990, Jamus ba ta amince a hukumance ba da  raba iyaka da kasar Poland. Bugu da kari ma da  garin Oder Neisse da wasu sauran wuraran da dama, Jamus din na tunanin yankinta ne Poland ta kwace mata, sai da Rasha da sauran kasashe kawaye suka matsa mata kaimi kana ta amince.