Yajin aikin gama gari a Najeriya. | Labarai | DW | 10.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gama gari a Najeriya.

Ƙungiyar kwadago a Tarayyar Najeriya ta dakatar da yajin aikin gama da ta ƙaddamar a fadin ƙasar.

default

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

Ƙungiyar ƙwadago a Tarayyar Najeriya ta ce za ta dakatar da yajin aikin da takaddamar a faɗin ƙasar bayan tattaunawar da ta yi tare da gwamnati. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar ya ce ƙungiyar za ta gudanar da wani taro a wata mai zuwa domin yin nazari akan ci-gaban da gwamnatin ta samu wajen biyan buƙatarta ta samun ƙarin albashi. A yau aikin bankuna da makarantu da kuma wani ɓangare na sufuri sun tsaya cik sakamakon yajin aikin da aka kuduri aniyar gudanarwa ciiin kwanaki. Ƙungiyoyin ma'aikata dai sun miƙa buƙatar kara karamin albashi daga euro 31 zuwa 61. Bankin duniya ya kiyasce cewa kashi 80 daga cikin ɗari na al'umar Najeriya ke samun albashin da ya yi ƙasa da euro ɗaya da rabi a kowace rana. Najeriya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'uma a Afirka, tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu arziƙin man fetur a duniya, bugu da ƙari kashin bayan tattalin arziƙin yammacin Afirka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita : Ahmad Tijani Lawal