Yajin aiki a Turai kan matsalar tattali | Labarai | DW | 14.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aiki a Turai kan matsalar tattali

Wasu ƙasashen Turai sun haɗe da Spain da Portugal wajen gudanar da yajin aiki da zanga zangar adawa da matakan tsuke bakin aljihu

Miliyoyin ma'aikata dake yankin kudancin nahiyar turai ne suka shiga yajin aikin nuna adawa da matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatocinsu suka ɗauka. Shugabannin ƙungiyoyin kwadagon dai sun bayyana waɗannan matakai na kara haraji da rage kuɗaɗe, a matsayin wata kafar daɗa tsananta matsalolin tattali da yankin ke fuskanta. Ma'aikata a ƙasashen Spain da Portugal dai sun kaddamar da wannan yajin aiki, a yayin da ƙungiyoyin kwadagon Girka, Italiya, Faransa da Belgium suka sanar da shirinsu na haɗewa a wannan yajin aiki ko kuma zanga zanga, a matsayin nuna goyon bayansu ga sauran ƙasashen da abun ya shafa. Harkokin sufurin motoci da jiragen ƙasa dai sun tsaya cik, a yayin da aka soke sauka da tashin jiragen sama a ƙasashen na Spain da Portugal. Kazalika makarantu da ma'aikatun gwamnati sun kasance a rufe, a ɓangaren wannan rana ta ɗaukar mataki da goyon baya ga ƙasashen turai dake fama da matsalolin durkushewar tattali. Rahotani daga Madrid din ƙasar Spain dai na nuni da cewar, jami'an tsaro sun cafke 32 daga cikin masu zanga-zangar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu