Yadda ake tuki a manyan titunan Jamus
Jamus ta yi suna a duniya ba wai kawai a kan motocin da take kerawa ba, har ma da manyan titunanta masu inganci. Ga wasu daga cikin abubuwan da mutum ya kamata mutum ya sani, kafin ya fara tuki.
Sai inda mai ya kare
Kasa daya tilo a nahiyar Turai da ba a kayyade iya adadin gudun da mutum zai yi a wasu manyan titunanta ba. Jamus na da kyawawan manyan tituna da ake bai wa kula sosai, abin da ke sanya mutane sha'awar tuki a kansu. Mafi karancin shekaru da za a iya mallakar lasisin tuki a Jamus shekaru 17 ne, amma sai da dan rakiya. Sai dan shekaru 18, zai kiya samun lasisin tuki ba tare da shamaki ba.
Ka shirya wa cunkoso
Kididdigar kungiyar kula da ababen hawa ta Jamus ADC, ta nunar da cewa cunkoson ababen hawa a Jamus a shekara ta 2022 da 2021 na kama da juna. Ya karu da kaso 15 cikin 100 a 2016, idan aka kwatanta da 2015. Ya yawaita a kasar da za a iya kira karama, abin da aka alakanta da yawan ababen hawa a manyan tituna da kuma ayyukan gyaran hanya. Koda yake annobar corona ta sa mutane da yawa aiki daga gida.
Masu azarbabi
Ko da kananan tunanin cewa ka kure malejinka a babban titi, za ka ji tamkar ba ka sauri. Wasu direbobi a Jamus za su yi ta bibiyarka, har ma su yi kokarin wuce ka. Za ma su iya damunka da yi ma fitila, domin su tilastaka ka ba su hanya. Bai kamata ka tare hanyar da aka yi ta domin wucewa ba, amma ka da ka bari wani direba mai azarbabi ya cuzguna maka!
Murmushi ga na'urar daukar hoto!
Ka kula da na'urar lura da gudun direbobi! Ana amfani da su sosai a Jamus, a manyan tituna da ma na cikin gari. Ana dasa na'urorin a kusa da hanya, kuma sau tari suna daukar hoton ba tare da an sani ba. Da za ka yi gudun da ya wuce kima, za a aiko maka tara har gida hade da hotonka da na'urar ta dauka da kuma lambar motarka domin tabbatar da laifin da ka aikata.
Amfani da wayar salula: Haramun
Rike wayar salula a hannu a lokacin tuki, haramun ne. Idan aka kama mutum, za a ci tararsa Euro 100, tare da tarar ja maka jan layi daya a lasisisn tukinka. Hukuncin zai karu idan ka haddasa hadari, za ka iya rasa lasisinka. An kara yawan tarar a 2017. Sa na'urar daukar waya a mota ba tare da amfani da hannu ba ne mafita. Ana cin tarar mai tukin keke ma, a kan amfani da wayar salula yayin tuki.
Bayar da hanya domin kawo dauki
Haka abin yake idan ba a bayar da hanya ga motocin jami'an agajin gaggawa ba. Komai cunkoso, akwai bukatar samar da layi guda saboda motocin daukar maraasa lafiya da na 'yan sanda ko da ba a hango fitilarsu ba. Akasin haka, ka iya janyo tarar Euro 200 da kuma jajayen layuka a lasisin tuki. Ko wannen lokaci layin agajin gaggawa na tsakanin karshen bangaren hagu da sauran layukan da titi ke da su.
Saka alamomin gargadi
Akwai bukatar saka alamomin gargadi, yayin da abin hawa ya tsaya ko aka samu hadari. Wannan na nufin saka alama mai kalar fatar lemon zaki da kuma saka fitilar gargadi, tilas wadannan baubuwa su kasance cikin mota ko yaushe. Tilas a samar da akwati mai dauke da kayan kula da maras lafiya a matakin farko, cikin ababen hawa.
Tuki cikin yanayin maye
A Jamus haramun ne ga wadanda suka fara tuki da ma kwarrarun direbobi su sha barasa. Tilas ya kasance adadin barasar da direban mota ya sha bai wuce digo-sifili-biyar cikin 100 ba. Wanda ke tuka keke kuma, digo 16 cikin 100. Tara na farawa da Euro 500, zuwa jan layi a lasisi da ma dakatar da shi na tsawon wata guda. Kyakkyawar mafita: Kar ka sha barasa ka yi tuki!
Tayoyin lokacin kankara
Akwai bukatar tayoyin lokacin kankara da zarar hanyoyi sun yi santsi sakamakon dusar kankara ko kuma kankara kadai, a Jamus hakan ka iya faruwa tsakanin watan Oktoba da lokacin Easter. Tuki a hanyoyi masu santsi ba tare da tayoyin lokacin kankara ba, ka iya janyo cin tara da kuma jan layi a lasisi. Idan ba a sa tayoyin lokacin kankara ba, inshora ka iya kin daukar nauyi idan hadari ya afku.
Yanayin hutawa
Domin gujewa tuki a manyan hanyoyin Jamus da ma na cikin gari, ka dauki matakin hutu. Dauki lokacinka, ka da ka bari gajiya ta mamaye ka. Baya ga haka ma, la'akari da yanayin jiragen kasa masu tsada da kuma tsarin ababen hawa a kasar, ba lallai ka bukaci daukar motarka ba. Kana iya hawa jirgin kasa, kafafuwanka su huta!