Ya kamata fararen hula su jagoranci gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso | Siyasa | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ya kamata fararen hula su jagoranci gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso

Kasashe makotan Burkina Faso na hankoron ganin fararen hula sun jagoranci gwamnatin rikon kwaryar da za ta shirya zabukan kasar masu zuwa.

A jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta ce tana goyan bayan matsayin kungiyoyin kasa da kasa na Afirka dama duniya wajen ganin sojojin Burkina Faso, sun baiwa farar hula damar tafiyar da mulkin rikon kwaryar da za tashirya zaben maido da kasar bisa tafarkin demokiradiyya da hanzari, ta kuma ce tana fatan lamarin da ya wakana ga mulkin tsohon shugaban kasar Balise Compaore zai zama wani babban darasi ga duk wasu shugabannin musamman na kasashen nahiyar Afrika da ke da niyyar yin tazarce a kan karagar mulkin kasashensu ba bisa ka'ida ba

Ministan kula da harakokin kasashen waje na kasar Nijar Malam Bazum Muhammed ne lokacin wani taron 'yan jarida na musamman da ya kira a birnin Yamai, ya bayyan wannan matsayi na gwamnatin Nijar, dangane da halin da ake ciki a makobciyar

Burkina Faso Zida mit Oppositionsanführer Diabre 02.11.2014

Zida da jagoran 'yan adawa Diabre

kasa ta Burkina Faso. Ministan dai ya ce ba tun yau ba ne gwamnatin Nijar ke bin abubuwan da ke wakana a Burkina Faso sau da kafa.

Juyin Juya hali ne a Burkina Faso?
Wannan abun da wasu suka kira sabon juyin juya halin da ya kai ga
korar tsohon shugaban kasa Balaise Compaore daga karagar mulki bayan mulkin kama karya na shekaru 27 ya zo ne a daidai lokacin da shugabannnin wasu kasashen Afrika da aka zaba a demokiradiyyance ke shirin neman yin tazarce a kasashensu.

Dubban 'yan asalin kasar Burkina Faso ne dai ke rayuwa yanzu haka a Nijar, kuma wasunsu sun bayyan mana ra'ayinsu da ma fatansu a kan halin da kasar tasu ta ke ciki: "Yau a kasarmu Burkina ba dadi sai dai mu fatanmmu shi ne soji su yi hakuri su bar ma farar hula milki su kuma farar hula idan sun samu mulki kar su tsaya yin wata ramuwar gayya su zauna guri daya su yi sulhu a daina duk wasu kashe kashe domin maido da zaman lafiya a kasar".

Sauti da bidiyo akan labarin