Wani jirgin ƙasa na ƙasar Indiya ya yi hatsari a gabacin ƙasar | Labarai | DW | 28.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani jirgin ƙasa na ƙasar Indiya ya yi hatsari a gabacin ƙasar

Mutane 65 suka mutu a sakamakon hatsarin jirgin ƙasar da ya auku a ƙasar Indiya

default

Wani jirgin ƙasa na ƙasar Indiya

Wani abu da ya fashe a gabacin ƙasar Indiya, ya yi sanadiyar kaucewar wani jirgin  ƙasa daga kan hanyarsa. Jirgin wanda ya taso daga Bombai zuwa Cal-culta ya kuma ci karo da wani jirgin ƙasar da ke ɗauke da kayayakin yan kasuwa.

Mutane a ƙalla guda  65 suka mutu a sakamakon wannan hatsari da ake kyautata zaton cewa ƙungiyar yan tawayye na Maoiste sune umul-haba'isin aukuwar haɗarin.

Gidan Talabijin na ƙasar ya nuno hotunan tarkacen jirgin da ya yi kaca kaca, wanda kuma wasu da dama daga cikin fasinjojin suke sarƙe cikin tarkacen ,  

Ministan sufurin jiragen ƙasa na Indiya Mamata Banerjee, wanda ya tabbatar da cewa yan tawaye sune suka ɗana bam ɗin, ya shedda cewa a kwai yiwuwar samun ƙaruwar adadin mutane da hatsarin ya rutsa da su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.

Edita        : Abdullahi    Tanko  Bala.