Waiwayen shekara a Najeriya | Siyasa | DW | 31.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Waiwayen shekara a Najeriya

Mahimman batutuwa da suka faru a Najeriya a shekara ta 2014

Babu ko shakka shekara ta 2014 ta kasance wacce ke cike da kalubale ga mafi yawan al'ummomin Najeriya duk da cewa an samu ci-gaba a wasu fanonin na rayuwa.

Shekara ta 2014 ta kasance wacce ‘yan Najeriya ke yake tare da tagumi saboda irin abubuwan da suka faru a fanonin tattalin arziki, da siyasa da kuma batun tsaro in wasusnu suka girgiza wanzuwar kasar a shekaru 54 da samun yanci.

Fanin tsaro ya kasance kan gaba a abubuwan da suka faru a 2014 saboda yadda yake ci gaba da zama kadangaren baki tulu musamman yadda sojojin Najeriya ke gudu daga fagen fada da yayan kungiyar Boko Haram ke karbe garuruwa tare da shellar kafa daular Islama. Da ma yadda yadda a ranar 14 yadda a ranar 14 ga watan Afrilu aka sace yan matan makarantar sakandire ta Chibok su 219 wadanda har yanzu ba'a kaiga gano su ba duk kuwa da gangamin da 'ya'yan kungiyar Bringback our girls suke ci gaba da yi.

Zargin bankado salwantar tsabar kudi har dalla bilyan 20 na man fetir da tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar ya yi a watan Mayu ya kasance zargin cin hanci da masu halin bera ke mayar da baitimali a aljihunsa da ya faru a 2014.

Sai dai karbar bakuncin taron koli na tattalin arziki na duniya karo na 24 ya daga martabar Najeriya, wanda bayansa ne ma Najeriya ta sake sabunta matsayin tattalin arzikinta da ya nuna cewa it ace kan gaba a Afrika.

Taron kasa da aka gudanar ya kasance muhimmi saboda dadewar da aka yi ana jan kafa a kansa dama nuna tsoron zai rarraba kawunan alummar kasar.

Samamen da ‘yan sanda suka kai a majalisar dokokin Najeriya tare da fesa barkonon tsohuwa ga ‘yan majalisar ya zama babban al'amarin da ya faru a 2014 musamman hana shugaban majalisar Hon Aminu Tabuwal shiga abinda ya haifara da hayaniya.

A gefe guda kuma wasikar da Cif Obasanjo ya rubtawa shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ta sanya an hange su a rana.

Takadamar da sake neman takarar shugaban Najeriya Goodluck ya kasance daya daga cikin batutuwan da za a ci gaba da su a 2015 mai kamawa, a yayin da al'ummar kasar ke zura ido yadda za a gudanar da zabubuka a 2015 duk da matsalolin da ke tattare da rarraba katin zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin