1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuwela ta saki dan jaridar Jamus

Abdul-raheem Hassan MNA
March 16, 2019

Dan jarida Billy Six ya fito daga gidan yari a kasar Venezuwela bayan shafe watanni hudu a tsare kan zargin leken asiri, an kuma umarceshi bisa sharadin zai rika ziyartar hukumomi a kai a kai.

https://p.dw.com/p/3FATK
Deutschland Billy Six 2013
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Wata kungiyar kare 'yancin 'yan jaridu a Venezuwela ta tabbatar da sakin dan jaridar Jamus Billy Six da hukumomi suka tsare kan zargin leken asiri da yi wa gwamnati zagon kasa. Kungiyar Espacio Publico ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an saki dan jaridar ne bisa sharadin zai rika gabatar da kansa ga hukumomi duk bayan kwanaki 15 tare da haramta masa yin magana kan halin da ya shiga bayan da shafe watanni hudu a tsare a kurkuku. 

Billy Six dan jarida ne mai aiko da rahotanni na wata mujalla a Jamus, ya kuma shahara a rahotannin yankunan yaki cikin har da kasashen Libiya da Ukraine da Siriya.