Ukraine ta kai hari a cibiyar man fetur na Rasha
November 4, 2025
Talla
Jiragen yakin Ukraine mara matuka sun kai hari wata cibiyar man fetur na Rasha, ma'aikatar tsaron kasar ta kakkabo jirage 85 a wani mataki na dakile hare-haren Ukraine ta sama. Rasha ta jadda da aniyar kare matatun man kasar da sauran cibiyoyin makamashi daga barazana.
A cigaba da kare kanta daga mamayar Rasha fiye da shekaru uku da rabi, Ukraine na kai hare-haren ramuwar gayya a yankunan Moscow, musamman a cibiyoyin masana'antu don rage kaifin tasirin sojojinta.
Hare-haren baya-bayan nan da Ukraine ke kai wa Rasha, na shafar yadda take fitar da man fetur da dizel wadan da kasar ke dogaro a kansu wajen samar da kudaden shiga.