1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta bukaci agajin kawayenta cikin gaggawa

April 8, 2024

Shugaban kasar Ukraine Volodymr Zelensky ya sake jaddada bukatar neman taimako makamai biyo bayan zafafa hare-hare da kasar Rasha ke kaiwa Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4eWhZ
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky
Shugaban Ukraine Volodymyr ZelenskyHoto: Ukrainian Presidency/abaca/picture alliance

Shugaban Zelensky ya ce dole ne kawayen Ukraine su tashi taye wajen ganin sun taimaka mata da makamai domin kare kanta daga mamayar Rasha. Ya ce ya kamata duniya ta san halin radadi da al'ummar Ukraine ke ciki dangane da mummunar hare-haren Rasha na luguden bama-bamai da kuma kai farmaki ba kakkautawa a birni na biyu mafi girma a Ukraine.

Karin bayani: Rasha ta sake kai hari kan tashoshin makashi a Ukraine

A wani jawabi da ya gabatar ta bidiyo, shugaban ya ce Rasha za ta iya galaba akan Ukraine idan har majalisar dokokin Amurka ta ki amincewa da tallafin kudin sayen makamai ba, wanda 'yan majalisar daga jam'iyyar Republican suka ki amincewa da kudurin.

Karin bayani: Jamus ta hana Ukraine makamai masu linzami