Ukraine na janye manyan takokinta na yaki | Labarai | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine na janye manyan takokinta na yaki

A wani mataki na yin biyayya ga yarjejeniyar baya-bayan nan da aka cimma kan rikicin gabashin kasar Ukraine, bangarorin biyu dai sun fara daukan kyawawan matakai.

A wannan Talatar ce sojojin kasar Ukraine za su kammala janye manyan tankokinsu na yaki daga yankin Lougansk da ke gabashin kasar, inda a cewar wani kakakin sojan kasar, nan zuwa karshen yinin wannan rana za su kammala wannan aiki kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a makon da ya gabata tsakanin bengarorin a birnin Paris na kasar Faransa ta tanada. Su ma dai daga nasu bangare 'yan awaran gabashin kasar masu goyon bayan Rasha, za su fara janye nasu manyna makamman daga ran 18 ga wannan wata kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Sai dai kamar yadda shugaban kasar ta Ukraine Petro Porochenko ya yi tsokaci a kai, a baya-bayan nan cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, 'yan awaran gabashin kasar ta Ukraine sun dage zabukan kananan hukumomin da suka shirya na ran 18 ga wannan wata na Octoba da kuma na ran daya ga watan Novemba mai zuwa, kamar yadda yarjejeniyar baya-bayan nan ta kasar Faransa ta tanadar.