1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na fama da karancin makamashi

November 26, 2022

Yankuna da dama a kasar Ukraine na fama da karancin ruwan sha sakamakon hare-haren da Rasha ke kai wa cibiyoyin samar da wutar lantarki masu yawa na kasar.

https://p.dw.com/p/4K772
Hoto: Evgeniy Maloletka/AP/picture alliance

Shiyoyi 15 na kasar Ukraine ne a yanzu ke fama da karancin ruwan sha sakamakon yadda Rasha ke tsananta hare-hare a kan tashohin samar da wutar lantarki da dama na kasar.

Kamfanin samar da makamashin lantarkin Ukrenergo, ya ce rabin yankunan kasar ne kadai yake iya sama wa wutar.

Har i zuwa jiya Juma'a ma dai ko a Kyiv babban birnin kasar ma dai, rabin gidaje ne suka samu wuta.

Sai dai ofishin magajin garin birnin, ya ce kashi biyu bisa uku na samun makamashin dumama gidaje a wannan lokaci na tsananin sanyi na hunturu.

Haka ma a cewar hukumomin an shawo kan matsalar karancin ruwa a Kyiv din da ke fadar gwamnatin kasar.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai na gargadin cewa hare-haren na Rasha a kan cibiyoyin samar da makamashi na iya zama babbar barazana ga rayuwar 'yan Ukraine din.