Turkiyya ta dauki sabon salo a hulda da kasashen waje | Siyasa | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turkiyya ta dauki sabon salo a hulda da kasashen waje

Lokacin da ya haye karagar mulki a watan Mayu, Firaministan Turkiyya ya sanar da cewar lokaci ya yi da kasarsa za ta yi gyaran manufofinta na ketare.

Recep Tayyip Erdoğan und Benjamin Netanjahu KOMBI

Recep Tayyip Erdogan da Benjamin Netanjahu

Turkiyyan a 'yan kwanaki da suka gabata ta inganta dangantakarta da Isra'ila da Rasha, dangantakar da ta jima da yin tsami. Kasar ta Turkiyya da ta saba samun baki masu yawon bude ido musamman a lokacin bazara, na fuskantar koma baya a yawan wadanda ke ziyartar kasar. Kuma masu otel-otel da 'yan kasuwa na bayyana rashin jin dadinsu na samun 'yan yawon shakatawa musamman 'yan Rasha da kan yi dandazo a irin wadannan wurare na bakin ruwa.

Sai dai a wannan shekarar an samu Jamusawa masu yawa da suka tafi hutu a Turkiyya, amma ba kamar na shekarun baya ba. Wannan ne ya sanya kananan 'yan kasuwa da ke dogaro da 'yan yawon bude idon yin korafi. Ga dai abin da wani mai tukin tasi ke cewa:

Wladimir Putin Recep Tayyip Erdogan Russland

Vladimir Putin da Recep Tayyip Erdogan

"Wannan ya kasance yanayi mafi muni da ba mu taba ganin irinsa ba sama da shekaru 20 da suka shige. Domin ba mu da komai, ba ma iya sauke nauye-nauyen da suka rataya a wuyanmu. Kuma hukumomi ba sa taimaka mana."

Miliyoyin Rashawa 'yan yawon bude ido ne dai ke tafiya zuwa Turkiyya kafin dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu. Inda suke jin gajiyar rana da iskar bakin ruwa. A kan haka ne al'ummar kasar suka fara kira ga gwamnati da ta gyara manufofinta na ketare tare da sake farfado da dangantakar diplomasiyya da kasashen da ba sa dasawa, domin farfado da sashen kula da yawon bude ido.

Firaministan Turkiyyan Binali Yildirim dai ya yi kokarin kwantar da hankalin al'ummarsa, bayan da Turkiyya da Rasha suka dinke barakar da ke tsakaninsu.

Türkei Treffen Yildirim und Erdogan

Yildirim tare da Erdogan

"A zahiri mun fara ganin ingantuwar dangantaka. Abin da zai biyo baya shi ne tattalin arziki, wanda ke nufin harkokin yawon bude ido ma za su bunkasa."

A daya hannun kuma farfado da dangantakar diplomasiyya tsakanin Turkiyya da Isra'ila shi ma zai je nesa ba kusa ba wajen bunkasa harkokin yawon bude ido, daura da iskar gas da ake saran za ta fara kai wa Turkiyyan. Oguz Celikkol shi ne tsohon jakadan Turkiyya a Isra'ila.

"A shekara ta 2008, sama da Yahudawa dubu 500 ne suka je hutu a Turkiya. A bara kuwa dubu 200 ne kadai. Amma ko shakka babu yanzu yawan zai sake kai na 2008."

Kazalika kasashen biyu za su cigaba da alaka a fannin tsaro. Kasashen biyu dai na da ra'ayi guda kan Iran da ke tasiri a rikicin Siriya.

Sauti da bidiyo akan labarin