Turkiyya ta ce ba ta cinikayya da ′yan IS | Labarai | DW | 01.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta ce ba ta cinikayya da 'yan IS

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai yi murabus in Rasha ta bada shaidun da ke nuna cewar Ankara na yin cinikin mai da 'yan IS.

Turkiyya dai ta ce ta na yin cinikin dukannin mai da ma iskar gas da ta ke amfani da shi ne ta halastaciyyar hanya kuma ba daga hannun 'yan ta'adda ta ke saye ba.

Erdogan na wadannan kalamai ne a wani mataki na musanta zargin da Rasha ke yi wa gwamnatinsa na alaka ta cinikayya da IS musamman ma dai danyen mai wanda ake zaman guda daga cikin abubuwan da ke samawa kungiyar kudaden shiga.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin Ankara da Moscow wadda ta samo aslinta bayan da sojin Turkiyya suka harbo jirgin yakin Rasha a makon jiya bisa zargin keta sararin samaniyarta ba bisa ka'ida ba.