1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta tanadi wajen karbar hatsi daga Ukraine

July 27, 2022

Matakin na zuwa ne kwanaki biyar bayan da Rasha da Ukraine suka kulla yarjejeniyar fitar da alkama da sauran kayan abinci daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine, matakin da ka iya saukar da farashin kayan abinci a duniya.

https://p.dw.com/p/4Ej1G
Ukraine-Krieg | Abkommen über Export von ukrainischem Getreide
Hoto: OZAN KOSE/AFP

Turkiyya ta kaddamar da wata cibiya da ta ware domin tarbar kayan abincin da aka yo fitonsa daga Ukraine a karkashin yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine, a karon farko tun bayan da Rasha ta yi wa Ukrane kutse. 


Ministan tsaron Turkiyya  Hulusi Akar ne ya kaddamar da cibiyar da za a rika sauke kayan abincin da aka fito da su ta tekun Bahr Aswad daga tashoshin jiragen ruwa guda uku na kasar Ukraine 


Hakan ta tuni ta sanya farashin alkama ya fara sauka a kasuwannin duniya. To sai dai harin makamai masu linzamin da Rasha ta kai wa tashar jirgin ruwa ta Odesa, daya daga cikin inda ake fitar da kayan abincin na Ukraine, ya haifar da shakku kan yiwuwar dorewar wannan yarjejeniya.