Turkiya ta zargi Rasha da takalar fada | Labarai | DW | 30.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta zargi Rasha da takalar fada

Mahukuntan kasar Turkiya sun sanar da cewa wani jirgin saman kasar Rasha kirar SU-34, ya ketara sararin samaniyar kasar ba bisa ka'ida ba.

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu

Rahotanni sun nunar da cewa tuni ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Turkiyan ta yo sammacin jakadan Rasha a kasar kan wannan batu. Ma'aikatar kasashen ketare ta Turkiyan dai ta sanar da cewa jirgin yakin na Rasha ya ketara sararin samaniyarta duk kuwa da gargadin da na'urar hangen jiragen sama ta kasar ta yi masa. Wata sanarwa da ma'aikatar ta fira ta nunar da cewa ketara mata sararin samaniya ba bisa ka'ida ba, da jirgin yakin ya yi na nuni da cewa Rasha na son takalarta fada ne. Idan dai za a iya tunawa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, tun bayan da sojojin Turkiyan suka harbo wani jirgin saman yakin Rashan a kan iyakar Turkiyan da Siriya a kwanakin baya.