Turkiya ta fara kai hare-hare a siriya | Labarai | DW | 24.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta fara kai hare-hare a siriya

Gidan talabijin din kasar Turkiya ya ruwaito cewa tankokin yakin Turkiya sun tsallaka kan iyakar kasar Siriya, a karon farko da kasar ta daura damarar yaki da 'yan kungiyar ta'addan IS a yankin arewacin Siriya.

Turkiya ta kaddamar da yaki da IS

Turkiya ta kaddamar da yaki da IS

Tun da fari dai jiragen yakin Turkiyan da na Amirka, sun yi luguden wuta kan maboyar 'yan IS din a yankin Jarabulus da ke arewacin kasar Siriyan. A 'yan kwanakin baya-bayan nan dai Turkiyan ta zargi kungiyar ta IS da kai hare-hare cikin kasarta. Koda a karshen wannan mako ma dai sai da wani harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 54 a yayin da suke halartar shagalin bikin aure a Turkiyan, harin kuma da mahukuntan na Ankara suka dora alhakinsa kan kungiyar ta IS.