Turai ta bukaci kawo karshen yamutsin Burundi | Labarai | DW | 14.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai ta bukaci kawo karshen yamutsin Burundi

Shugabanin kungiyar Turai sun bukaci daukar kwararan matakai domin magance yamutsin kasar Burundi bayan mutuwar mutane da yawa a sakamakon harin da aka kai kan wani barikin sojojin kasar.

Kimanin mutane 87 suka mutu a kasar ta Burundi bayan wasu hare-hare da 'yan tada kayar baya suka kai a kan wani barikin sojoji a ranar Jumma'a wadanda ake kyautata zaton masu adawa da tazarcen Shugaba Pierre Nkurunziza ne.

A yayin taron ministocin kasashen Turan da suke gudanarwa a birnin Brussels, kantomar harkokin wajen EU Federica Mogherini ta yi nuni da cewar:

Sun tuntubi shugabanin kungiyar Afrika da su shiga a dama da su wajen tattauna batun zaman lafiyar Burundi bisa jagorancin yankin.