Turai: Shekaru 75 da kawo karshen yakin duniya na biyu | Labarai | DW | 08.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai: Shekaru 75 da kawo karshen yakin duniya na biyu

Yayin da nahiyar Turai ta cika shekaru 75 bayan yakin duniya na biyu a wannan ranar Juma'ar 8 ga watan Mayu, yanayin ranar ya kasance cikin alhini sakamakon annobar coronavirus wacce ta haifar da soke bukukuwa a bana.

Nan gaba kadan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier za su ajiye furanni a Neue Wache, dandalin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu da danginsu yayin yakin duniyar na biyu gabanin jawabi na musamman  daga shugaban tarayyar ta Jamus.

Batun kebe rana ta musamann a Jamus don tunawa da yakin da ya haifar da asarar rayukan sama da mutane miliyan 50 na cigaba da fuskantar muhawara a Jamus.