1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai na cikin tsaka mai wuya kan Iran

Abdullahi Tanko Bala USU
May 17, 2018

Shugabannin kasashen Turai na tattaunwa a taron koli a birnin Sofia na kasar Bulgeriya domin daukar matakin martani ga ficewar Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

https://p.dw.com/p/2xtOY
Bulgarien EU-Westbalkan-Gipfel in Sofia
Hoto: Reuters/S. Nenov

Shugaban taron kuma shugaban kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk ya bude jawabi a madadin kasashe 28 na Tarayyar Turan da kakkausar lafazi, inda ya soki shugaban Amirka Donald Trump game da janyewa daga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka rattaba wa hannu, kan shirin nukiliyar Iran da kuma karin kudin fito kan karafa da gorar ruwa daga Turai.

Donald Tusk yace "idan aka dubi matakin shugaba Trump mutum na iya yin tunani yace, da abokai irin wadannan baka bukatar karin wasu makiya. To amma a zahirin gaskiya, ya kamata nahiyar Turai ta yi wa shugaba Trump godiya, saboda ya yaye mana dukkan wasu shakku. Ya sa mun fahimci cewa idan kana bukatar taimako to ka waiwaya hannunka mai kafada. Wajibi ne kasashen Turai su yi iya karfinsu su kare yarjejeniyar cinikayya Turai da Amirka, duk da wannan hali da aka shiga a yanzu, a lokaci guda kuma mu kasance cikin shirin yanayin da za mu dauki mataki da kan mu"

Bulgarien EU-Balkan-Gipfel in Sofia | Merkel & Vucic
Hoto: picture alliance/AP Photo

Shugabanin Jamus da Faransa suma sun yi tsokaci kan takaddmar da ke tsakanin Tarayyar Turan da Amirka, a taron kolin kasashen Turan na birnin Sofiya. Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace Tarayyar Turai za ta kare kamfanoninta da ke huldar kasuwanci da Iran, daga takunkumin da Amirka ta sake kakaba wa Tehran kan shirinta na nukiliya. "Yana da muhimmanci a baiwa kananan kamfanoni damar zabin inda suke so su yi kasuwanci ba tare da tarnaki ba, bisa irin muradinsu na kasuwanci. Kamfanoni na da damar yin zabi, musamman kamfanoni wadanda ba su fadada kasuwancinsu a Amirka ba."

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a nata bangaren ta jaddada bukatar dage harajin kudin fito na kashi 25 ckin dari da shugaba Trump ya dora kan karafa daga kasashen Turai da kuma harajin kashi 10 cikin dari akan gorar ruwa bisa togaciya ta dalilai na tsaron kasa. "Mun fayyace matsayin mu kan batun kasuwanci, musamman cinikayya da Amirka. Kuma mun dauki matsayi guda. Muna bukatar a tsame kasashen Turai daga wannan karin harajin, amma a shirye muke mu tattauna akan samun masalaha yadda za a rage tarnaki ga harkar cinikayya."

Taron kolin shugabannin Turai da takwarorinsu kasashe shidda na yankin Balkan, yana kuma duba yadda za su karfafa dangantaka a tsakaninsu.