1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sassauta dokar kulle a Turai

Zainab Mohammed Abubakar
May 2, 2020

A Spain bayan kwanaki 48 na zaman gida a wani mataki na kare yaduwar cutar, a wannan Asabar din ce aka fara barin mutane su fita waje domin shan iska.

https://p.dw.com/p/3bgw8
Spanien Coronavirus Lockerung Ausgangssperre
Hoto: Getty Images/C. Alvarez

Yawan mutanen da cutar Covid 19 ta kama a yanzu haka ya haura miliyan uku a duniya baki daya, daga cikinsu 237,137 sun rasa rayukansu, a cewar alkaluman kamfanin dillancin labaru na Reuters.

Yaduwar cutar ta Corona a gidajen kurkukun Indiya da ke cunkushe dai, ya sa mahukuntan daukar matakin sakin dubban fursunoni, bayan kwararru a fannin lafiya sun nuna damuwa kan yadda cutar zata yadu kamar wutar jeji, saboda yanayin cunkoson gidan mazan.

Tun daga ranar 14 ga watan Maris nedai aka garkame al'ummar Spain miliyan 47 a gidajensu, a karkashin wata dokar kulle mai tsanani, inda ake barin mutane su fita waje kawai saboda sayen kayan abinci ko magani.