Turai da Amirka sun amince da tattaunawa kan rikicin Libiya | Labarai | DW | 22.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai da Amirka sun amince da tattaunawa kan rikicin Libiya

Manyan kasashen duniya sun yi na'am da shirin tattaunawa kan rikicin jagoranci a Libiya a wani mataki na kawo karshen tashin hankali a kasar.

Manyan kasashe na Turai da Amirka, sun yi marhabin da shirin tattaunawar neman maslaha kan rikicin da bangarori biyu masu jayayyar ikon gwamnati ke yi a kasar Libya, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani don samun gwamnatin hadaka a kasar.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen Faransa da Jamus da Italiya da Spaniya da Burtaniya da kuma Amirka, sun yi kira ga masu tattaunawa kan wannan batu da cewar su shiga zauren sulhu da manufar dinke barakar kasar ta Libiya, musamman kokarin ganin an tsagaita budawa juna wuta ba tare da wani jinkiri ba.

Yayin dai da ake shirin zama nan gaba a kasar Maroko, gwamnatin kasar ta Libiya wadda kasashen duniya suka yarda da ita, ta ce an kaddamar da hari a birnin Tripoli, a kokarin da ake kai na kwace birnin daga ikon mayakan tawayen da ke da goyon kungiyar nan ta IS.