1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tura kudade daga Jamus lokacin bukukuwa

Binta Aliyu Zurmi YB
December 24, 2018

Daga cikin kasashen da suka fi samun kudaden 'yan Afirka daga kasashen waje sun hada da Najeriya da ke kan gaba sai Senegal da Ghana. Aika kudi a karshen shekara kan zama wani kalubale.

https://p.dw.com/p/3Aadv
Symbolbild Euro-Geldscheine
Hoto: picture-alliance/imageBroker/S. Klein

Mutane da yawa za su iya fahimta matsalar karancin kudi musamman ma a irin wannan lokaci na karshen shekara da ke zuwa da bukukuwa idan ya kasance daidai lokacin da mutum ke son aika wa iyalansa kudi a Afirka. Damuwar na da yawa sannan ba duka 'yan Afirka da ke zaune a Turai ne ke iya jure damuwar 'yan uwa da abokan arziki da ke gida ba.

Ibrahim dan Najeriya ne kuma a ganinsa yana da matukar muhimmanci mutum ya fara duba iyalansa da ke nan Jamus kafin ya ce zai aika da kudi gida musamman ma a irin wannan lokacin da abubuwa da yawa ke faruwa kuma akwai karancin kudi.

Cikin mutanen da Dw ta tattauna da su a kan wannan batu wasu sun nuna damuwar yadda iyalansu da ke Afirka ba sa fahimtar yadda aika masu kudi ke da wahala. Kamar yadda wata mata 'yar kasar Ghana da ta bukaci a boye sunanta ta bayyana cewa mutane da dama a Afirka idan aka tura masu kudi ko godiya ba sa yi sai dai dai kai mai kudin ka kira don sanin ko sun isa don kai ka san zafinsu.

Weihnachtsshopping Geschenke Kaufrausch
Karshen shekara lokacin faranta rai ga mutaneHoto: Imago/R. Peters

Wannan kalubale da 'yan Afirka mazauna Turai ke fuskanta ba a kan ma’aikata kadai ya tsaya ba, hatta wadanda ba sa aiki da suma daga gwamnati ke samun na cin abinci na fuskantar hakan. Sani Abatcha shi ma daga Ghana ya bayyana yadda mutanen da ya baro a gida ke bukatar taimako, sai dai ba ya iya taimaka masu yadda ya kamata don ba shi da shi, kasancewar har yanzu ba ya aiki. 

Daba Zambake 'yar asalin kasar Senegal ce da ta dade tana zaune a nan Jamus ta san wannan matsalar da matsin da 'yan Afirka ke ciki na jin maganar aikawa da kudi gida ne daga wajen abokanta, saboda ita sai za ta gida ta ke siyan tsaraba, don ‘yan uwanta a gida na aiki. Duk yadda wahalar aikawa da kudi gida mutane na tausaya ma halin da su ka baro 'yan uwansu a ciki. Kuma idan har rayuwa a kasashen Afirka da ke fama da talauci ba ta canza ba, hakan nan komai wahala mutane za su ci gaba da aikawa da kudin don taimakon 'yan'uwan su.