Tunawa da yakin duniya na daya a Turkiya da Armeniya | Labarai | DW | 24.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunawa da yakin duniya na daya a Turkiya da Armeniya

A Armeniya bikin na zama na tunawa da kisan Armaniyawa miliyan daya da rabi a shekarun 1915 zuwa 1916 .

Armenien Völkermord Messe in einer Kirche in Eriwan

Malaman addini a lokacin bikin tunawa da mamata

A ranar Juma'ar nan Turkiya na karbar bakuncin shugabannin duniya dan tunawa da wadanda suka rasa rayukansu shekaru dari bayan fafatawar Gallipoli da aka yi a yakin duniya na daya. A bikin da ke tura sakon neman sulhuntawa cikin takaddamar da ta dabaibaye tsohuwar daular ta Turkiya.

Dubun dubatar al'umma ne dai suka rasa rayukansu a lokacin wannan yaki da ya dauki tsawon watanni tara ana fafatawa tsakanin dakarun daular ta Turkiya da ake kira Ottoman Empire a Turance da ke samun goyon bayan kasar Jamus, da kawancen dakarun kasashen Ostareliya da Birtaniya da New Zealand .

A yanzu dakarun da suka kwanta dama a lokacin wancan yaki daga bangaren dakarun daular ta Turkiya da dakarun kawancen na binne a makabartu da ke makotaka da juna a mashigar teku ta Gallipoli a yammacin Turkiya, abin da ke zaman ginshikin tunawa da sulhuntawar da aka yi tsakanin bangarori biyu da ke gaba da juna.

A wannan biki da za a sha shagali a bakin teku, shuban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan zai karbi bakuncin firaministan kasar Ostareliya Tony Abbott da firemiyan New Zealand John Key da Yarima Charles na Birtaniya da dansa.

Haka lamarin yake a bangaren al'ummar kasar Armeniya suma na bikin tunawa da shekaru dari na tunawa da kisan kimanin Armaniyawa miliyan daya da rabi a shekarun 1915 zuwa 1916 a lokutan gushewar daular Turkiya da akafi sani da Ottoman Empire a turance.