Tuddan tsira a wasu yankunan Siriya | Labarai | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tuddan tsira a wasu yankunan Siriya

Kasashen Rasha da Iran da Turkiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta taka birki ga sojojin Amirka wajen kai samame a wasu yankunan da za a kebe a matsayin tudun muna tsira a kasar Siriya.

Syrien Interview Bashar al-Assad mit französischen Journalisten in Damaskus (Reuters/Sana)

Shugaban Siriya, Bashar al-Assad.

Wakilin Rasha Alexander Lavrentyev ne ya bayyana wannan matakin kwana guda bayan kasashen Turkiya da Iran sun cimma matsaya a taron tsagaita wuta da aka gudanar tsakanin 'yan tawayen Siriya da bangaren gwamnati a birnin Astana. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterrers ya yi na'am da wannan mataki, amma ya bukaci a fadada dokar hana jiragen Rasha da Turkiyya kai hare-hare a kan yankunan Idlib da Latakia da Aleppo da kuma Hama da aka kebe a arewacin Siriya. Wannan mataki na zama wani yunkuri na rage tashin hankali da ke sanadiyar rayukan fararen hula, sakamakon yawan kai hare-hare da suka tilasta daruruwan al'umma rabuwa da matsugunansu.