Faransa : Nicolas Sarkozy ya shaki iskar 'yanci
November 10, 2025
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarcozy, ya fita daga gidan yarin Santé, inda ake tsare da shi, bayan da kotun daukaka kara ta sallame shi a wannan Litinin.
Tsohon shugaban Faransa ya rasa wata daraja ta kasa
Nicolas Sarkozy mai shekaru 70, ya shafe fiye da kwanaki 20 a gidan yari, bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan wakafi, bisa samunsa da laifin karbar kudi daga Libiya don cin moriyar yakin neman zabe.
Babban mai shigar da kara a Faransar ne ya bukaci kotun daukaka kara ta birnin Paris, ta saki tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy, wanda aka tsare a gidan yari, kuma shaidun gani da ido sun ce an fita da Nicolas Sarkozy daga gidan kason a cikin wata mota mai bakin gilashi, tare da rakiyar 'yan sanda.
Nicolas Sarkozy zai yi shekaru biyar na zaman gidan yari
Tsohon shugaban kasar Faransan ya kafa tarihi, inda ya kasance shi ne na farko a daga cikin tsoffin shugabannin kasar da aka yankewa hukuncin dauri a gidan kaso.
Shugaba Sarkozy ya tsinci Talatarsa a Laraba a Faransa
Guda daga cikin lauyoyinsa Jean-Michel Darrois, ya bayyana wa kafafen yada labarai cewa duk da yake Sarkozy, ya kasance mutum mai karfin hali da jajircewa, tsarewar da aka yi masa ta jefa shi cikin azaba da ciwon zuci mai tsanani.
An hango Nicolas Sarkozy a zaman shari'ar ta bidiyo, yana cewa zama a kurkuku "abu ne mai wuya kuma mai matukar wahala".