Tsohon shugaban Jamus ya bayyana a kotu | Labarai | DW | 14.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Jamus ya bayyana a kotu

Sama da watanni shida bayan murabus daga mukaminsa, a wannan alhamis din ce Wulff ya bayyana a gaban kotu, domin kare kansa daga zargin karbar rashawa.

Wulff da ke kasancewa shugaban Jamus na farko da ya bayyana a gaban kotu kan badakkalar cin hanci dai, ya lashi takobin wanke kansa daga wannan zargi da ake masa. Ana zargin tsohon shugaban na Jamus mai shekaru 54 da haihuwa da amince wa alfarmar biyan wani bangaren kudaden balaguron da wani abokinshi ya yi masa, a wata ziyara da ya kai birnin Munich shekaru biyar da suka gabata. A wancan lokacin shi ne fraiministan jihar Lower Saxony. Abokin nashi dai ya kasance mai shirya fim, wanda alfarmar da ya yi wa tsohon shugaba Wulff, da ya kunshi euro 700 ke zama martani ne na taimaka masa da ya yi wajen tallata fina finansa. Wannan dai shi ne kadai zargin da ya rage a kan tsohon shugaban na Jamus, bayan kammala binciken wasu laifuka da suka hadar da karbar alfarma da rance daga wajen wasu abokansa masu hannu da shuni.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh