Tsohon shugaban Jamus Walter Scheel ya rasu | Labarai | DW | 24.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Jamus Walter Scheel ya rasu

Fadar shugaban kasa Joachim Gauck ita ta fitar da wannan sako a ranar Laraban nan, inda ta ce tsohon shugaban kasar ya rasu bayan lokaci mai tsawo na rashin lafiya.

Deutschland ehemaliger Bundespräsident Walter Scheel, FDP

Walter Scheel tsohon shugaba a Jamus

Tsohon shugaban kasar Jamus Walter Scheel da ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita Yammaci da Gabashin Jamus ya rasu yana da shekaru 97.

 

Fadar shugaban kasa Joachim Gauck ita ta fitar da wannan sako a ranar Laraban nan, inda ta ce tsohon shugaban kasar ya rasu bayan lokaci mai tsawo na rashin lafiya.Shi dai tsohon Shugaba Scheel ya kasance mai ra'ayi na ganin hadin kan Turai ta tabbata. An haife shi a ranar takwas ga watan Yuli shekarar 1919 birnin Solingen, da ke a Yammaci na Jamus.