Tsohon shugaban Jamus Herzog ya rasu | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Jamus Herzog ya rasu

Roman Herzog mai shekaru 82 ya mulki Jamus tsakanin shekarar 1994 zuwa 1999. Sannan ya taba shugabantar kotun tsarin mulki kasar

Tsohon shugaban kasar Jamus Roman Herzog mai shekaru 82 da haihuwa ya rigamu gidan gaskiya. Shi dai marigayin ya kasance shugaba na farko da aka zaba a Jamus bayan da kasar ta sake hadewa, inda ya mulki tsakanin shekarar 1994 zuwa 1999. Sannan ya taba shugabantar kotun tsarin mulki na kasar.

Roman Herzog wanda dan jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ne ya yi ruwa da tsaki a zamanin mulkinsa don ganin cewar Jamus ta gudanar da sauye-sauye da za su inganta tattalin arzikinta. Shugaba Joachim Gauck da ke kan mulki ya jinjina wa marigayi Herzog dangane da dora kasarsa kan kyakkyawar turba da ya yi.

"Roman Herzog ya kasance mai yawan bayyana kalmomin da suka dace. Sannan ya bayar da gudunmawa wajen karfafa fahimta tsakanin 'yan siyasa da talakawa.".