Tsarin masarautar Katsinan Maradi | Zamantakewa | DW | 08.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tsarin masarautar Katsinan Maradi

Masarautar Maradi na da dadaden tarihi a fuskar masarautu na Nijar,masarautar na da tsari na zabe wanda gungun mutane hudu ke zaben sarkin wadanda suka hada da Galadima da 'Yandaka da Kaura da kuma Durbi.

Mai martaba Sultan Ali Zaki sarkin Maradi ya bayyana cewar kakanni da iyaye haka ake tafiyar da zaben masarautar garin Maradi. Maradin wace ake kira da sunan Katsinan Maradi na da alaka da Katsina ta Najeriya kafin zuwan turawa su raba iyaka tsakanin Najeriya da Nijar. Kasuwanci ya habaka a garin Maradi abin da ya sa birnin ya yi suna sossai.

Sauti da bidiyo akan labarin