1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spaniya da Faransa na fama da wutar daji

Binta Aliyu Zurmi
July 17, 2022

Gobara dajin a kasashen Spaniya da Faransa na karuwa saboda tsananin zafi da kasashen nahiyar Turai ke fuskanta

https://p.dw.com/p/4EGIU
Frankreich | Waldbrände Rehion Bordeaux
Hoto: SDIS 33/AP/picture alliance

A Faransa sama da mutum dubu 14 ne gobarar dajin ta tilasta wa barin matsugunansu, tsananin zafin da ya haura maki 40 a ma'aunin Celciues a wasu kasashen, masana na cewar ya buso ne daga nahiyar Afirka.

Tun bayan da zafin ya tsananta a kasar Spaniya an sami mutuwar mutane 360 a tsukin kwanaki biyar.

Gobarar daji a wannan shekarar ta yi saurin zuwa, lamarin da ke kara nuna kamarin sauyin yanayi .