Tsaiko a filin jiragen sama na Hamburg | Labarai | DW | 12.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaiko a filin jiragen sama na Hamburg

Rahotanni na nuni da cewa an samu tsaiko na sama da sa'a guda a filin sauka da tashin jragen sama na kasa da kasa da ke birnin Hamburg a kasar Jamus.

Tsaiko a filin sauka da tashin jiragen sama na Hamburg

Tsaiko a filin sauka da tashin jiragen sama na Hamburg

Tsaikon dai ya samu ne sakamon wata gurbatacciyar iskar gas da ta mamaye filin, inda tuni aka kwashe fasinjoji da ma ma'aikatan filin jirgin zuwa waje mai tsaro. Kawo yanzu dai babu masaniya kan jirage nawa ne tsaikon da aka samu ya shafi zirga-zirgarsu a filin sauka da tashin jiragen saman na Hamburg da ke zaman filin sauka da tashin jiragen sama mafi tsufa a duniya da har yanzu yake aiki, kana na biyar mafi girma a Jamus din. Fasinjoji a kallah 68 ne aka tabbar da cewa sun jikkata ta hanyar sarkewar numfashi, kana wasu da dama suka yi korafin zafin idanu da kaikayi da kuma tari.