Tsagerun Niger Delta sun yi watsi da tayin sulhu | Labarai | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagerun Niger Delta sun yi watsi da tayin sulhu

A Najeriya kungiyar 'yan tawayen Niger Delta Avengers ta yi fatali da tayin neman sulhu da gwamnatin kasar ta yi mata a farkon wannan mako.

Kungiyar ta sanar da wannan matsayi nata ne a cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a wanann Laraba, inda ta ce babu wata tattaunawa da ta soma da wani kwamiti, kuma idan har gwamnatin Najeriyar ta ce ta soma tattaunawa da wasu Kungiyoyin 'yan tawayen na yankin na Niger Delta, to Kungiyoyin na wakiltar kansu ne kadai.

A ranar Litanin din da ta gabata ce sakataran kasa mai kula da harakokin man fetur na Najeriyar Emmanuel Ibe Kachikwu ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin Najeriya za ta dakatar da matakan soja da ta dauka a yankin na Niger Delta a baya bayan nan, har na tsawon mako daya zuwa biyu domin hawa tebirin tattaunawa da kungiyoyin 'yan tawayen yankin.