Tsagaita wuta a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 08.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Dubban mutane ne dai suka hallaka sama da miliyan ɗaya aka tilasta musu kaurace wa muhallansu a rikicin ƙasar, wacce ba ta daɗe da samun 'yancin kanta ba.

'Yan tawaye a Sudan ta Kudu a ranar Asabar din nann sun bayyana cewar ɓangaren gwamnati shi ya fara karya yarjejeniyar da suka ƙulla ta tsagaita wuta, wannan jawabi na fitowa ne sa'oi kaɗan bayan da dukkanin ɓangarorin biyu suka yi alƙawarin kawo ƙarshen fadan da suka fafata da juna kusan shekara guda.

Ƙungiyar tarayyar Turai ta EU da Amirka da suka yi ta ƙoƙari wajen ganin wannan jaririyar ƙasa bat a faɗa cikin mafi munin ruɗani ba tuni suka ƙakaba wa dukkanin ɓangarorin biyu takunkumi saboda yawaita karya yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙullawa, ta farko da aka ƙulla a watan Janairu.