1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi amai ya lashe kan amfani da karfi a Greenland

Binta Aliyu Zurmi
January 22, 2026

Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa a zauren taron Davous ya bayyana cimma yarjejeniyar mai gamsarwa a kan tsibirin Greenland, kuma ya janye aniyarsa ta amfani da karfi don mallakar tsibirin.

https://p.dw.com/p/57DBP
Schweiz Davos 2026 | US-Präsident Donald Trump spricht beim Weltwirtschaftsforum in Davos
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Wannan matakin na Trump da ke cike da ban mamaki na zuwa ne bayan wata ganawa da ya yi da sakatare janar na kungiyar kwanacen tsaro ta NATO, Mark Rutte, wanda ya shaida wa Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tattaunawar ta yi kyau matuka, amma har yanzu akwai sauran aiki a gaba.

Kazalika a sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Socials, Trump ya ce sun samar da yarjejeniyar a kan Greenland, kuma a sabili da haka zai soke harajin da ya sha alwashin dora wa kasar Denmark daga ranar 1 ga watan Fabrairu da kuma wasu kasashen Turai da suka tura dakarunsu zuwa Greenland da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus.

Kakakin NATO Allison Hart ya ce Denmark da Greenland da Amurka za su tabbatar da cewa Rasha da China ba za su taba samun tasiri ta fuskar tattalin arziki ko ta soja a Greenland ba, wata mahimmiyar damuwa ta Trump.

 

Karin bayani: Trump ya jadadda matsayinsa na neman mallakar Greenland