Harajin Donald Trump kan kasashen Turai na yamutsa hazo
January 18, 2026
Faransa ta ce Shugaba Donald Trump ne zai fi ji a jiki idan har ya fara aiwatar da matakin haraji ga kasashen Turai da suka nuna adawa kan shirinsa na karbe tsibirin Greenland.
Da take magana da kafafen yada labarai, ministar harkokin noma na kasar Faransa Annie Genevard, ta ce "Donald Trump zai iya rasa abubuwa masu yawa idan ya aiwatar da karin harajin." Ta kara da cewa "Irin wadannan matakai ka iya cutar da tattalin arzikin Amurka, da assasa tashin farashin kayayyakin more rayuwa ga 'yan kasar, sannan ya kawo cikas ga kasuwancin duniya."
Sojojin Turai na shiga yankin Greenland don samar da kariya
Kungiyar injiniyoyi ta Jamus, ta roki tarayyar Turai da ta yi amfani da dokar nan da ta ba ta damar kare nahiyar ga duk kasar da ta yi wa kasashen barazana a kan Amurka. Dokar mai suna ‘Anti‑Coercion Instrument’ an samar da ita ne don kare nahiyar kan duk wata barazanar da ka iya shafar kasashen Turai kan batun tattalin arziki ko kare manufofinsu daga waje, a wani mataki na ramuwar gayya.
Trump ya sanya harajin kashi 25 ga abokanan kasuwancin Iran
A wannan Lahadi, shugabar gwamnatin Italiya Giorgia Meloni, ta sanar da cewar ta tattauna da shugaban Amurka, Donald Trump, tare da sanar da shi abubuwan da take gani game da wannan takaddama, tana mai cewa, "hasashen kara haraji kan kasashen da suka zabi ba da gudummawa wajen tsaron Greenland, a ganina kuskure ne, kuma ba shakka ban yarda da hakan ba."
Trump ya sha alwashin karbe iko da Tsibirin Greenland ka ta wace hanya
A ranar Asabar ne Shugaba Trump ya sanar da kakaba haraji na kaso 10 cikin 100 kan kasashen Turai da suka yi adawa da yunkurinsa na karbe yankin Greenland, da suka hada da Denmark da Norway da Sweden da Faransa da Jamus Burtaniya da Netherlands da kuma Finland, kuma matakin zai ci gaba har zuwa lokacin da za a cimma yarjejeniyar sayar masa da yankin na Greenland.