1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran da sa'o'i 24

April 5, 2026

Shugaban na Amurka ya wallafa cewa "kuna da nan da Talata, karfe 8:00 na yamma agogon Gabashin Amurka."

https://p.dw.com/p/5Bipt
Trump ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran da sa'o'i 24
Trump ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran da sa'o'i 24Hoto: Alex Brandon/AFP

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fada a ranar Lahadi cewa ya ƙara wa’adin da ya bai wa Iran da sa’o’i 24 domin ta cimma yarjejeniya ta buɗe mashigar Hormuz, ko kuma ta fuskanci munanan hare-hare kan muhimman wurarenta na makamashi.

Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa "kuna da nan da zuwa Talata, ƙarfe 8:00 na yamma agogon Gabashin Amurka!”

Trump: Za mu iya daina kai hari Iran nan da makonni 2-3

Sabon wa’adin, wanda ya yi daidai da ƙarfe 0000 agogon GMT na ranar Laraba, na nufin Iran za ta samu ƙarin yini guda a wa'adin Trump na farko domin ta amince a daidaita, ko kuma ta fuskanci barazanar lalata tashoshin wutar lantarki da gidajenta.

Tun bayan fara hare-haren bamabamai da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta toshe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar mai da iskar gas a duniya.

Trump ya jinkirta kai wa cibiyoyin lantarkin Iran hari

Iran ta ce ko a jikinta da barazanar Trump, kuma ana taba mata tashoshin lantarki to gaba daya na Gabas ta Tsakiya za su durkushe.