1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta mika daftarin tsagaita wuta ga Iran

March 25, 2026

Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa Iran da wani shirin tsagaita bude wuta ta hannun Pakistan, wadda ke da kyakkyawar alaka da bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/5B3Y0
Trump na da kwarin gwiwar samun daidaito da Iran
Trump na da kwarin gwiwar samun daidaito da IranHoto: Kyle Mazza/TheNews2/IMAGO

Amurka ta gabatar wa Iran da wani shirin zaman lafiya mai kunshe da sharudda guda 15, a kokarin kawo karshen yaki, ciki kuwa har da bukatar Teheran na ta mika daukacin sinadarin uranium da ta tace da kuma bude mashigin Hormuz. 

Jaridar New York Times ta Amurka da kuma gidan talabijin din Isra'ila Channel 12, sun ruwaito cewa gwamnatin Donald Trump ta isar da wadannan bukatu ga Iran ta hannun Pakistan, wadda ke da kyakkyawar alaka da bangarorin biyu.

Gidan talabijin na Channel 12 ya ruwaito wasu majiyoyi uku da suka tsegunta masa cewa wasu daga cikin sharuddan da aka gindaya wa Iran sun hada da dakatar da daukar nauyin kungiyoyin Hezbollah da Hamas, sannan za a kayyade adadin makamai masu linzamin da za ta iya mallaka da kuma zangon da su iya ci.

Hakazalika an kuma tanadi sassauta wa Iran takunkuman kasa da kasa da aka kakaba mata, tare da ba ta goyon baya kan shirinta na amfani da makamashin nukiliya domin ayyuka da ba su shafi kera makamai ba.

Ko da yake har yanzu Washington ba ta yi karin waske kan wannan batu ba, amma Trump ya bayyana kwarin gwiwar yiyuwar cimma yarjejeniya da Teheran.

Shugaba Trump ya janye shirin kai hari a cibiyar wutar Iran

Straße von Hormus 2026 | Thailändischer Frachter Mayuree Naree nach Angriff in Flammen
Hoto: Royal Thai Navy/Handout/AFP

Sabon fata ga arzikin duniya duk da ci gaba da yaki

Iran ta kaddamar a wannan Laraba da jerin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan makwabtanta da kuma Isra'ila, yayin ita ma Isra'ilar ta ci gaba da yi barin wuta a kan birnin Tehran da kuma kasar Lebanon, duk kuwa da mika tayin tattaunawar tsagaita wuta da Amurka ta yi.

Rahotanni na nuni da cewa kalaman Trump kan yiwuwar cimma daidaito da Iran sun sa farashin mai ya sauka a wannan ranar Laraba, yayin da kasuwannin hannayen jari suka fara farfadowa a nahiyar Asiya.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta gaskata cewa ta samu sakon tayin tattaunawa daga Amurka ta hanyar ''kasashe abokanta'' sai dai ta karyata batun cewa shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf na wakiltarta a tattaunawar.

Wasu rahotannin kuma daga kafafen yada labarain Amurka sun nuna yiwuwar Washington ta tura karin sojoji lema 3,000 zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake ci gaba da gwabzawa ba tare da alamar kakkautawa ba.