Trump ya hau kujerar na ki a kan Saudiyya | Labarai | DW | 17.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya hau kujerar na ki a kan Saudiyya

Shugaba Donald Trump na Amirka, ya hau kujerar na ki dangane da matsayin da majalisun kasar suka cimma kan dakatar da taimakon Saudiyya a yakin kasar Yemen.

Wannan ne dai karo na biyu ke nan da shugaba Trump ke amfani da karfinsa na iko, wajen bijire wa matsayin majalisun dokokin na Amirka.

Matakin hawa kujerar ta na ki da Mr. Trump ya yi, bai zo wa duniya da mamaki ba saboda alakar kasar da masararutar Saudiyya

Amincewar majalisun biyu dangane da taimaka wa yakin na Yemen a baya dai, wani abu ne da ke zama na tarihi.

Hakan ya kasance ne duk da tabbacin da hukumar leken asirin Amirkar ta bayar dangane da hannun Yerima mai jiran gadon Saudiyya, Muhammad Bin Salman, da kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi, a bara.