Trump: Saudiyya ta bari a kai agaji a Yemen | Labarai | DW | 07.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump: Saudiyya ta bari a kai agaji a Yemen

Amirka ta yi kira ga kawarta Saudiyya, da ta gaggauta kyale shigar kayan agajin jin-kai kasar Yemen mai fama da yaki a halin yanzu.

Kiran da shugaba Donald ya yi, ya bukaci a kyale shigar abinci da ruwan sha da kum amagunguna ne ga kimanin mutane miliyan bakwai a Yemen din, da Makalisar Dinkin Duniya ta ce tana gab da shiga mummunan yanayi. Sai dai fa shugaban na Amirka bai nuna bukatar da hare-haren bama-baman da Saudiyyar ke jagoranta a kasar ba.

Sabon fada ya barke a Sanaa babban birnin kasar ta Yemen, tsakanin 'yan tawayen Houthi da masu goyon bayan gwamnati, bayan kashe tsohon shugaba Ali Abdallah Saleh ranar Litinin da ta gabata. Saudiyya da kawayenta dai sun kaddamar da wani kamfe na kakkabe mayakan na Houthi a wannan birni.