Trump na ziyarar aiki a kasar Birtaniya
June 3, 2019Talla
Ana ganin tsokacin Shugaba Trump gabannin isowarsa Birtaniya kan dambarwar Brexit zai tada kura a ziyarar, bayan da ya ce tsohon ministan harkokin wajen Birtaniyar Boris Johnson zai zama kyakkyawar zabi da zai maye Firaminista Therasa May. Shugaban na Amirka ya shawarci wanda ake sa rana zai zama Firaminista na gaba da ya fice daga EU ba tare da cimma yarjejeniya ba, kuma ya ki biyan EU kudin rabuwa.
Matakin na Trump na shan suka daga 'yan adawa inda magajin garin Landan Sadiq Khan ya kwatanta kalaman Trump da mara kan gado. Ana sa ran cewa dimbin masu zanga-zangar yin tir da Trump kan rashin mutunta yarjejeniyar kare muahalli za su fantsama kan tituna yayin ziyarar ta Trump.