1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu: Zan dama da mata da matasa

Ahmed Salisu
May 29, 2023

Sabon shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin damawa da mata da matasa a gwamnatinsa, inda ya ce zai samar da guraben aiki ga matasa.

https://p.dw.com/p/4Rvxg
Nigeria Einweihung des neuen Präsidenten Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

A jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar kama aiki, Bola Ahmed Tinubu ya ce matasa da mata ne ginshinkin al'umma don haka zai yi aiki kafada da kafada da su, sannan zai samar musu da gurben aiki don yaki da zaman kashe wando.

Baya ga batu na samar da aikin yi ga mata da matasa, sabon shugaban na Najeriya ya sanar da janye tallafin man fetur tare da shan alwashin gyara darajar Naira a kasuwannin chanji inda ya ce za a samar da farashi na bai daya wajen chanjin Naira din a kasar.