Bola Ahmed Tinubu dan siyasa ne daga jihar Legas da ke kudancin Najeriya. Tun bayan da kasar ta koma a 1999 ya kasance ne a bangaren adawa.
Tinubu ya taka rawa wajen hadewar wasu jam'iyyu da suka kai ga samar da jam'iyyar APC mai mulki wadda ta samu nasara a zaben shugaban kasar da ya dora Muhammadu Buhari kan gadon mulki.