Tawagar Jamus ta isa kasar Amirka
October 30, 2013Talla
Wata tawagar manyan jami'an kasar Jamus ta isa birnin Washington na kasar Amirka, domin neman karin bayani kan zargin satar sauraron wayar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wanda ake yi wa jami'an leken asirin Amirka.
Steffen Seibert kakakin Merkel, ya ce wakilan tawagar za su gana da hukumomin leken asiri na Amirka da kuma fadar gwamnatin kasar. Sannan akwai wata tawagar ta biyu da za ta isa kasar ta Amirka, duk kan wannan batu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu