1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin kudaden da 'yan Afirka ke aika wa zuwa gida

Daniel Pelz | Abdullahi Tanko Bala
May 23, 2017

A kasashe da dama na Afirka, kudaden da jama'ar su da ke zaune a kasashen waje suke aika wa gida suna da matukar muhimmanci wajen samun kudin shiga.

https://p.dw.com/p/2dRCr
Symbolbild Scheingeschäfte
Hoto: Imago

 

Sai dai kuma kaso mai yawa na wadannan kudade suna tafiya ne ga bukatun gida na daidaikun jama'a, lamarin da ma'aikatar raya kasashe ta Jamus ke fatan kawo sauyi a cikinsa. Ga Sylvie Nantcha wadda ke zaune a nan Jamus, ta ce wannan abu ne na nuna sanin ya kamata, a kowane wata ta kan turawa mahaifiyarta  kudi zuwa Kamaru. " Kasashenmu ba mu da tsari na tallafi da gwamnati kan bai wa jama'a ko kuma tsari na Inshorar lafiya".

Nantcha ta kwashe shekaru 24 tana zaune a nan Jamus kuma dukkan wannan tsawon lokaci dangantakarta da iyalinta tana nan daram. Iyaye suna da hakki a kan ya'yansu kamar yadda suma ya'yan suke da hakki na kula da iyayen su. To amma idan kana zaune a kasar waje nauyin ya fi girma saboda ana daukar cewa kana da hali. Haka dai yawancin 'yan cirani daga Afirka da ke zaune a Jamus suke yi. Nantcha ta tattauna da wasu 'yan ciranin kusan dubu daya kuma kashi 90 cikin dari daga cikin su sun ce suna aike wa da kudi zuwa gida zuwa kasashen su na asali. A bisa alkaluma na ma'aikatar raya kasashe ta Jamus kimanin Euro biliyan daya da miliyan dari biyu 'yan Afirka suke aike wa gida a kowace shekara, yayin da a daya bangaren taimakon raya kasa da jamus din ke bayar wa ga Afirka yake Euro biliyan daya da rabi.