1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar kafa gwamnatin hadaka a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
March 13, 2023

Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu na kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa domin jawo abokan hamaiya na jamiyyun adawa a dai dai lokacin da ake fuskantar rarrabuwar kawuna.

https://p.dw.com/p/4Ocvg
Zababben shugaba Bola Tinubu
Zababben shugaba Bola TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Duk da nasarar da zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben da aka yi a kasar, rarrabuwar kawuna na addini da ma yanki na ci gaba da zama babban kalubale ga siyasar kasar da ma gwamnatin da za'a kafa nan da watanni biyu masu zuwa. Abin da ya sanya yunkuri da ma hasashe na kafa gwamnatin hadin kan kasa a Najeriyar da zababbane shugaban kasar ke son yi. Wannan mataki ya haifar da tunani da ma fata daga alummar kasar a yanzu.

Atiku Abubakar na PDP
Atiku Abubakar na PDPHoto: Radeno Haniel/AP/picture alliance

Tun bayan da ya samu nasarar lashe zaben na Najeriya da ya kasance cike da kace-nace a kansa, zababben shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamiti don zwarcin  manyan ‘yan takarar da suka yi hamaiyya amma ya tikasu da kasa, koda yake sun da ja a kan nasarar. Shin wane tasiri wannan zai iya yi ga siyasar Najeriyar da ma gwamnatin da ake shirin kafawa a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, lokacin da Tinubun zai dare karagar mulkin Najeriya da ya dade yana kishirwar ganin haka?

Zababben shugaban Najeriyar da ke da salo na nima lokacina ne a barni in dana na fusknatar kalubalantara da manyan abokan hamiyyarsu biyu ke yi a kotu, bisa tabbabar nasara da ya samu, inda a yanzu ake share fage don tattake wuri a kotun daukaka kara.

A lokutan baya dai Najeriyar ta ga irin wannan salon a kafa gwamnatin hadin kasa inda aka jawo jamiyyun adawa tare da ba wasu mukami.

Peter Obi na LP
Peter Obi na LPHoto: Katrin Gänsler/DW

A wata zantawa da shi tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar da ya yi takara da zababben shugaban Najeriyar yace in an aiko mashi da goron gayyata zai duba tare da shawara ga jamiyyarsa ta PDP. Za'a sa ido a ga yiwuwar faruwar haka a siyasar Najeriyar mai cike da sarkakiyar gaske.