Tashe-tashen hankula a Najeriya da siyasar Burundi | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Tashe-tashen hankula a Najeriya da siyasar Burundi

Yawaitar hare-hare a Najeriya da rikicin siyasar Burundi na daga cikin batutuwan nahiyar Afirka da jaridun Jamus suka mayar da hankali kai a wannan mako.

A labarin da ta buga game da tashe-tashen hankulan a Najeriya jaridar Berliner Zeitung ta ce zubar da jini a cikin watan azumin Ramadan a Najeriya, inda masu ta da kayar baya na kungiyar Boko Haram suka sauya dubarun kai hare-hare suna masu mayar da hankali kan munanan aiyukan ta'addanci. Jaridar ta ce a cikin watan Mayu rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa tana dab da murkushe kungiyar Boko Haram, kuma hakika hare-haren sun yi sauki. To amma yanzu murna ta koma ciki domin aiyukan masu ikirarin jihadin sun yi muni a cikin watan nan na Ramadan fiye da a lokutan bayan, ba bu kuma alamun sararawa nan gaba kadan.

Dole a sauye dubarun yaki da Boko haram

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga labari game da hare-haren na Boko Haram da ta ce sun yi muni yanzu.

Ta ce kama daga Zariya ya zuwa Jos da Potiskum da Kano kai da ma sauran yankuna a arewacin Najeriya, ta'asar kungiyar ce ta wanzu, inda 'ya'yanta ke kashe mutane babu kakkautawa. Suna kai hari a kan masu ibada a masallatai da coci-coci da wuraren cin abinci da sauran wuraren haduwar jama'a. A cikin kwanaki takwas da suka wuce mutane fiye da 200 suka rasu a arewacin Najeriya sakamakon aiyukan ta'addancin Boko Haram. Yanzu haka dai sojoji da 'yan sanda ba sa iya samar da cikakken tsaro. Saboda haka dole ne sojojin Najeriya da dakarun kasashe makwabta su sake dubarun yaki da Boko Haram. Samun hadin kan jama'a yana da muhimmanci. Wani muhimmin aiki ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shi ne sake maido da yardar jama'a ga dakarun tsaro. Sai dai ba zai cimma hakan cikin makonni kalilan masu zuwa ba.

Kira ga dage zaben shugaban kasa a Burundi

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Burundi ne tana mai cewa kasashe makwabtan Burundi sun yi kira da a dage zaben shugaban kasar kana aka kafa wata gwamnatin hadin kan kasa, sannan sai ta ci gaba tana mai cewa.

Kwanaki kalilan gabanin a gudanar da zaben shugaban kasa a Burundi kasashen gabashin Afirka makwabtan Burundi na kara matsin lamba a kan shugaba Pierre Nkurunziza. Jaridar ta ce ko da yake shugabannin kasashen Kenya da Ruwanda da Yuganda da kuma Tanzaniya ba su fito karara suka soki matakin shugaban na Burundi na neman wa'adin mulki karo na uku ba, abin da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar abin kuma da ya janyo rikicin siyasar kasar tsawon watanni, amma a taron kolin da suka yi kan kasar ta Burundi a birnin Dar-es-Salam karkashin kungiyar kasashen gabashin Afirka, shugabannin sun ba wa Nkurunziza shawara da ya dage lokacin gudanar da zaben daga ranar 15 ga watan Yuli zuwa 30 ga wata. Suka ce muhimmin abu shi ne kafa gwamnatin hadin kan kasa da za ta kunshi wakilan 'yan adawa da suka kaurace wa zaben. Sai dai bisa ga dukkan alamu wannan kira bai samu karbuwa ba, domin Nkurunziza ya ci gaba da yakin neman zabe.